Koriya ta Arewa za ta mika makaman nukiliya

Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong-Un ya sanar da Shugaba Vladmir Putin na Rasha cewa ya amince ya kwance damarar makaman nukiliya.

Shugaban ya bayyana haka ne a lkacin da yake karbar goron gayyata don ya ziyarci Rasha daga Shugaban kasar Vladmir Putin.

An shirya ziyarar ce domi karfafa dangantaka tsakanin kasashen biyu.

Shugaba Putin ya kebe kansa da kasarsa daga yunkurin diflomasiyya tsakanin Koriya ta Arewa da kasashen China da Amurka da kuma Koriya ta Kudu.

 

 

Amma da alama Rasha na son taka wata muhimmiyar rawa, a daidai lokacin da Kim Jong un ke kokarin sauya siyasar yankin.

Shugaba Vladmir Putin na Rasha ya mika goron gayyatar ga Mista Kim Jong un ne ta hannun ministan harkokin kasashen waje Sergey Lavrov.

Shugaba Kim ya amince ya ziyarci Rasha zuwa karshen wannan shekarar.

Wannan matakin da ya dauka zai nuna wa Amurka cewa Koriya ta Arewa na da muhimman kawaye, kuma idan taron da aka shirya yi tsakaninsa da shugaba Trump ya watse, to yana da zabi.

Shugaba Kim ya kuma fada wa Sergey Lavrov cewa a shirye yake ya kwance damarar makaman nukiliya a yankin Koriya, amma ya fi so a bi abin daki-daki.

Wannan matsayin ba zai yi wa Amurka dadi ba, wadda ke son Koriya ta Arewa ta mika dukkan makamanta gaba daya domin a ba ta tallafin da zai bunkasa tattalin arzikinta.

Soyez le premier à commenter

Poster un Commentaire

Votre adresse de messagerie ne sera pas publiée.


*