FIR’AUNONIN MASAR TA DAURI

MASAR KYAUTAR NILU

Kufalar kogin Nilu (Nile Valley)  na ‘daya daga cikin wurare na farko na wayewar kan yan adam. Masani Herodotus ‘dan ‘kasar Girka, tun lokaci mai tsawo ya kira Masar a matsayin kyautar kogin Nilu saboda dalilai kamar haka; kogin Nilu ne mafi girma a kogunan duniya, tsawonsa ya kai kilomita 6671. Ya taso ne daga tafkin Victoria ya malalo ta Uganda ya biyo ta Sudan sannan ya shigo kasar Masar ya malala ya fa’da tekun Mediterranean. Idan an dubi Masar za a lura cewa kusan dukanta hamada ne ba don kogin Nilu da ya ratsa ta cikinta ba. Ratsawar kogin Nilu ne ya sa kufa’dar kogin  ta zama mai matu’kar ni’ima ta fuskar shuke-shuke da noman rani. Duk shekara, mutanen wannan wuri kan dogara ne ga turbaya mai taki da kogin kan amayar ta hanyar yin ambaliya ta yadda ‘bangarorin kogin biyu za su wadatu da taki domin yin noman rani da na damina. Ta haka mazauna wurin ke samun wadatuwar abinci har ma su sayar ga wasu ‘kasashe. Wannan damar ce ta bada samuwar wayewar kai a wurin tun lokaci mai tsawon gaske.

ADDININ MISRAWAN DAURI

Misrawan dauri mutane ne masu addini. Ma’ana suna bin dokokin addinsu sau da ‘kafa. Sai dai su ba mutane masu bautawa Ubangiji guda ba. Suna da iyayen giji da dama, duk da cewa suna daukar shi kansa Fir’auan a matsayin Ubangiji. A kowane babban birni akwai mabautu. Kowane birni na da ubangijinsa, haka ‘kauyuka da gidaje, sai dai akwai ubangijin da kowa yake bi. Wasu daga cikin Iyayen gijin Misrawan dauri sun ha’da da;

Amun-Ra                      Ubangiji-Rana
Osiris                           Ubangijin Matattu
Isis                               Matar Osiris
Horus                           ‘Dan Osiris
Anubis                          Ubangijin Jana’iza
Ma’at                            Uwargijiyar Gaskiya
Thoth                            Ubangijin Rubutu
Sekhmet                       Uwargijiyar Ya}i.
Ptah                             Ubangijin Halitta
Mut                               Uwargijiyar Sama’u kuma uwar Fir’auna

Tunda suna bautar Iyayen giji ne da dama, a

wasu

lokuta wasu Iyayen giji suna zama muhimmai fiye da wasu. Alal misali Amun ko Amon jaramin Ubangiji ne, sai a sabuwar masarauta, bayan an dawo da babban birnin daular Thebes sannan ya zamo muhimmin ubangiji. Lokacin babban birnin yana Memphis babban ubangijin Misrawa a lokacin shi ne Ptah.

MUTUWA DA HISABI

“Jinjina a gareka Ubangijina Osiris! Zan tsira da gangar jikina har abada. Ba zan ru’be ba, ba zan zama abincin tsutsotsi ba; Ina tabbace, Ina raye, Ina da kuzari na, na tashi cikin salama, kayan cikina ba su ru’be ba, idanuwa na ba su lalace ba, ba a raba kaina da wuyana ba, gangar jikina  za ta tabbata, ba za ta shu’de ba” Wannan wani bayani ne na karanto maku daga cikin Littafin Matattun (Book of the dead) ]’dya daga cikin manyan bayanan da Masar ta dauri ta bar mana na dangane da yadda Misrawa suka ‘dauki mutuwa. Masu ilmin kufai sun gano cewa a cikin kowane kabari, akwai wasu rubuce-rubuce da ake yi, wa]anda manufarsu ita ce ta taimakawa mamaci ya isa lahira cikin nasara. Shi wannan ba saukaken littafi ba ne, a ainihin gaskiya ma masani Lepsius ne ya sawa tattararrun bayanan littafin matattu wanda ya buga a 1842.

Misrawan dauri sun yadda cewa in an mutu za a yi wa mamaci hisabi. Misali, in mutum ya mutu ana kyankyame gawarsa ne domin ya ji da’din yin sabuwar rayuwar lahira. To, bayan an yi bayanan nan na rubutu a kabarinsa wanda ake ganin kamar shine fasfon tafiya, sai kuma a kai ruhin mutum wurin da zai yi bayanin ayyukan da ya yi a rayuwar duniya. Misali mutum zai yi bayani kamar haka “ban tauye ma’auni ba, ban hana jariri shan mama ba, ban karkatar da hanyar ruwa ba, ban tauye ha}}in maraya ba, ban kashe kowa ba..”  da sauransu. Daga nan sai a ]auko zuciyar mamaci a sa ta a sikeli. A hannu guda na sikelin kuma sai a sanya gashin kaza ko na agwawa ko wani tsuntsu a auna. Idan gashin ya rinjayi zuciyar mutum, to ya haye kenan, in kuwa zuciyar mutum ta rinjayi gashin nan to mutum ya ka’de har ganyensa kenan.

SARAUTAR FIR’AUNA

Da farko ya dace mu gano asalin kalmar Fir’auna. Daga ina ta samo asali, kuma me take nufi. To ita dai kalmar Fir’auna ta samo tushe ne daga harshen Misrawan dauri. Ita dai kalmar Fir’auna da (Ingilishi Pharaoh) tana nufin ‘babban gida’ da harshen Misrancin Dauri. A dauri ana amfani da kalmar ne domin bayyan fadar Mai sarautar Misrawa. An fara amfani da kalmar ne domin kiran Masu Sarauta daga wajajen 1400BC. Ta ‘ko ‘karin kiran dan sarauta dan babban gida shi ne har kalmar ta juye ta zama taken sarauta. A tsarin addininsu, Fir’auna an ‘dauke shi a matsayin ‘dan Osiris, ‘daya daga cikin Iyayen gijinsu. Yana mulki ne a duniya a matsayin wakilin Osiris da sauran iyayen gijin Misrawa. Saboda haka, shi ne shugaban addini da kuma maya’ka. A wasu lokuta ma ana ‘daukar Fir’auna a matsayin wani ‘dan ‘karamin ubangiji tunda shi wakilin Osiris ne. Daga cikin fitattun Fir’aunonin da aka yi sun ha’da da Khufu da Zoser (Djoser) da Thutmose I da Thutmose II da  Akhanaten da Ramses II, da kuma  Fir’auniyaHatshepsut. Za mu yi bayani akan wasu daga cikin wa’dannan Fir’aunoni.

Mai Sarauta na farko da za a iya cewa shi ne ya kafa daular Masar ta Dauri shi ne Menes ko Nermer. Shi Menes shi ne ya ha’de garuruwan dake Kudancin kufa’dar kogin Nilu da kuma na Arewacin kogin Nilu. Ga jerin Gidajen Sarauta da kuma sunayen wasu daga cikin Fir’aunonin da aka yi a Masar daga gabanin samuwar Masarautu zuwa zamanin Girkawa da Rumawa.

ZAMANIN MULKIN FIR’AUNONIN MASAR

Kafin samuwar Masarautu         Kafin 3150 BC

Masaurautun farko-farko                         3150BC-2686BC           Gidajen Sarauta I -2

Tsohuwar Masarauta                              2686-2181BC              Gidajen Sarauta 3 – 6

Tsaka-tsaki na farko                                2181-2040BC              Gidajen Sarauta 6 – 11

Masarauta ta Tsakiya                             2040-1782BC              Gidajen Sarauta  11-13

Tsaka-tsaki na biyu                                 1782-1570BC             Gidajen Sarauta 13-17

Sabuwar Masarauta                                1570-1070BC               Gidajen Sarauta 18-20

1570-1293BC              Gidajen Sarauta 28

1570-1546                   Ahmose

1551-1524                    Amenophis I

1524-1518                   Tuthmosis I

1518-1504                   Tuthmosis II

1504-1450                   Tuthmosis III

1498-1483                   Hatshepsut

1453-1419                   Amenophis II

1419-1386                   Tuthmosis IV

1386-1349                   Amenophis III

1350-1334                   Amenophis IV(Akhanaten)

1336-1334                   Smenkhkare

1334-1325                   Tutankhamun

1325-1321                   Ay

1321-1293                   Horemheb

1293-1185                   Gidan Sarauta na 21

1293-1291                   Ramesses I

1291-1278                   Seti I

1279-1212                   Ramesses II

1235-1224                   Merneptah

1185-1070                   Gidan Sarauta na 20

1182-1151                   Ramesses III

Tsaka-tsaki na uku                                   1070-664BC                 Gidajen Sarauta na 21-25

Masarautun }arshe-}arshe                         664-332 BC                   Gidajen Sarauta na 26-31

Zamanin Girkawa-Rumawa                     332BC-395AD               Gidajen Sarauta na 26-31

(SarakunanTalamawa Ptelemies da na Rum)

 

FIR’AUNA KHUFU DA ZOSER

Yanzu kuma sai gabatar da bayani akan wasu daga cikin wa]annan Fir’aunoni da suka gabata. Dole ne mu ambaci Fir’auna Khufu da Zoser koda a gurguje ne domin kuwa sune suka gina Dalar Dutse da aka ce yana daga cikin manyan abubuwan mamaki na duniyar dauri guda bakwai. Wa]annan Fir’aunoni na farko sune suka gina manyan abubuwan tarihi da har yanzu muke ta’kama da su a matsayin kayan tarihi. Dalar Dutse da Mutum-Zaki (Sphinx) abubuwa ne na ban al’ajabi. Misali Dalar-Dutsen da suka gina takai kafa479 a tsawo, ta ‘kunshi a ‘kalla bulo (wanda kowane ya kai ton 2) guda 2,300,000. Herodotus, masanin Labarin {asa da Tarihi ‘yan ‘kasar Girka ya ruwaito cewa, sai da mutane 100,000 suka yi shekaru ashirin suna gina shi. Tir’kashi, har yanzu abin da ‘daure kai, domin an kasa gano yadda aka gina su. Shi kuma Mutum-Zaki (watau Sphinx) ya kai }afa 66 a tsaye, tsawonsa }afa 189.

FIR’AUNA AKHANATEN

Babban dalilin da ya sa na za’bi in kawo bayani akan wannan Fir’auna shi ne, domin ya bambanta da saura. A baya mun gaya maku cewa, Misrawa na bautawa Iyayen giji da dama, babba a cikinsu kuwa shi ne Amun-Re. Fir’auna Amenophis III, shi ne mahaifin Fir’auna Amenophis IV. Mahaifiyar Amenophis IV kuma Sarauniyar Amenophis III sunanta Tiye.Amenophis III Basarake ne wanda ya yi fice ya kuma yi suna ta fuskar jarumtaka da mulki.

Lokacin da Amenophis IV yana yaro, watau yana ‘dan Sarki kenan, bai taso tamkar sauran ‘yan Sarki ba. Maimakon ya maida hankali wurin koyon dabarun ya’ki da kuma sauran al’amura na jarumtaka da mulki, shi ya fi damuwa ne da wasu abubuwa na dabam. Misali shi ya fi damuwa da halittun Ubangiji ma’daukaki. Ya fi damuwa da kallon Dinya da Agwagin ruwa ko kifaye.  Ya fi damuwa da kallon fitowar rana da fa’duwarta. Da sauran abubuwa na halitta.

A wannan lokaci, manyan malaman addini na Masar wa’danda ke zaune a birnin Thebes sun kasaita matu’kar gaske. Tun farkon farawar Sabuwar Masaurauta, su wa’dannan malamai kan sami dukiya mai yawa daga masu sarauta da kuma mutanen gari. Saboda haka, sai suka fara zama barazana ga Fir’auna Amenophis III. Wannan ya sa a lokacin ya fara tunanin yaya zai yi ya rage masu ‘karfi. Ta haka ne ya fara gina manyan Mutum-mutumansa wa’danda daga bisani ya fara jan hankalin a ri’ka bauta musu. Ta haka kenan ya fara janye mabiya Amun-Re kenan. A Birnin Thebes bautar Fir’auna ta fara kar~uwa sosai haka a kudancin Masar.

Lokacin da Amenophis IV ya zama Sarki, ya gaji mahaifinsa Amenophis III, sai ya fara nuna alamun yana da ra’ayin wani Ubangiji da ake kira Aten. Shi wannan Ubangiji ba shi da mabiya da yawa. A ta’kaice ma dai, ba a damu da bin wannan Ubangiji Aten ba. Ana cikin haka sai ya far a nisanta kansa daga bautar Ubangiji Amun (Amun-Re). Daga nan sai ya gina Mabautar Aten a Birnin Karnak, Sarauniya kuma Uwa Tiye ta rika tausawa ‘danta domin lura da cewa shi mutum ne wanda bai damu da duniya ba, kuma ga alama ba zai iya yin mulki yadda ya kamata ba, ta hanyar yin amfani da ‘karfin tuwo. Ba a tabbatar da cewa ko ta goyi bayansa ba bayan ya bayyana sabon ra’ayinsa na jaddada addinin Aten.

 A ta’kaice dai sai ya bayyanawa Misrawa cewa ya sauya sunansa daga Amunophis zuwa Akhanaten. Wanna sabon suna ya warware shi daga bautar Amun gaba ‘daya ya kuma li’ka shi da bautar Aten. Ma’anar sabon sunansa shine Aten ya wadatu da ni. To daga nan ne ya fara bayyana cewa Misrawa su daina bautar Iyayen giji barkatai. Su bautawa sabon Ubangijinsa watau Aten. A cewarsa Aten shi ka’dai za a bautawa kuma ba za a wakiltar da siffarsa ta hanyar gunkin mutum ko dabba ba. Shi kuma Akhanaten ba za a kira shi ko a bauta masa a matsayin Ubangiji ba. Duk wannan abu da ake yi mabiya Amun-Re ba su jin da’di. Don haka sai suka fara shirya masa ma’kar ’kashiya. Wannan ne ya sa ya yi hijira daga Thebes zuwa wani wuri tsakanin ta da Memphis (wani babban birni a Masar ta dauri). A daidai wannan lokaci ne ya auri wata mata mai suna Nafertiti, ba a da tabbacin ko ita wacece ko ‘yar wacece, sai dai ana kyautata zaton cewa kila ‘yar sarauta ce ita ma. Nafertiti ta yi imani da wannan sabon addini na mijinta ta kuma ba shi cikakken goyon baya

A cikin shekar sa ta shida ne a kan karaga ya tafi wurin da zai gina sabon birninsa wanda ya kira Birnin Ubangiji. A dai-dai inda ya tsaya don kafa wannan sabon birni, ba komai face wasu ‘yan gidajen da talakawa ke zaune ciki bakin gabar kogin Nilu. Akhanaten da kansa ya ce game da wurin “Na sami wannan wuri da bamallakar  kowa ba, ba na wani Ubangiji ko Uwargijiya ba ne, ba na wani yarima ko gimbiya ba ne, ba wanda zai ce nasa ne”  Ya kwana a tantinsa, da safe ya fito ya shata iyacin inda birnin zai tsaya, ya kuma sa masa suna watau AKHATATEN ma’ana Birnin Aten. Sannan ya yi bauta ga Ubangijinsa, bayan nan sai ya cewa wa]anda suke biye da shi “ Aten Ubangiji ne, shi ne ya umarce ni da in gina wannan birni” sannan ya ci gaba “Ga ubangiji na Aten zan gina wuraren bauta”

Bayan shekara biyu aka kamala ginin Akhataten suka dawo tare da iyalinsa da mabiyansa. Bayanan da aka samu sun nuna cewa, wasu sun biyo shi ne domin sun yi imani da shi, wasu kuma don su sami abin duniya suka yi ‘kaura tare da shi. Imaninsa da gaskiya watau Maat ya bambanta da na sauran Fir’aunoni da suka gabace shi. Ga AkhanatenMaat ba kawai tana nufin gaskiya tsurarta ba ne kawai, a’a,  in an ce Maat, ana nufin ne aikata gaskiya, barin munafunci da annamimanci, bayyan abubuwa a yadda suke. Wannan sabuwar manufa ta shafi yadda ake tafiyar da rayuwar yau da kullum ta wancan zamani. Ga ka’dan daga cikin yadda yake yabon Ubangijinsa Aten. (daga cikin rubuce-rubucensa)

Ayyukanka suna da yawa matu’ka Ya ubangiji tilo, babu wani tamkar sa Kai ka hallici duniya yadda ka soDa kai ka’dai ne tilo, Duk mutum, duka dabbobi na gida da na dawa Duk hallitta mai tafiya bias dugaduganta Duk abubuwan dake sama da halittu masu fiffika suna tashi

(shi Ya halicce su)

 Kai ka halicci’k}asashe har da }asar Masar Ka ajiye kowane mutum a wuri nasa daban Al’umomi suna harsuna da-ban daban Siffarsu ta jiki da launi sun banbanta Domin ka banbance tsakaninsu.

 

Ya haifi ‘diya mata  kamar su  Merytaten da Meketaten da Ankhhesenaten, sai dai bai haifi namiji ba.

Mabiya Iyayen giji da yawa sun ci gaba da shirya masa kulle-kulle da har daga baya dai ya sami ‘baraka da matarsa suka rabu. Daga bisani ya za’di mijin ‘diyarsa Makataten watau Samenkhkare ya zamar masa waziri. Da ga bisani dai ba za a iya cewa ga yadda ya ‘kare ba. To amma bayan fakuwarsa Semenkhkare ya zama Sarki. Bayan ya zama sarki sai ya bar Akhataten ya koma Thebes. Shi ma daga nan ba a san yadda ya ‘kare ba. Tutankhaten wanda shi ma surukin Akhanaten ne shi aka na’da sabon sarki, sai dai yana yaro sosai. Don haka, Ay wani babban kwamadan Akhanaten kuma mai bin addininsa shi ke mulki. Tutankhaten wanda ya maida sunansa Tutankhamun, bai da’de yana kan sarauta ya mutu yana ‘dan shekara 18. Don haka Ay ya haye karagar mulki. Shi ma saboda tsufa bai da’de ba ya mutu. Daga nan sai sarauta ta fa]a hannun Horembeb, wani babban kwamandan Masar.

Horembeb ya tabbatar da cewa an koma kan tafarkin addini da ake bi kaka-da kakanni. Da yake soja ne, sai ya ‘dora ‘kasar akan tsarin mulki irin na soja. Ya fara mulkin kama karya da gallazawa talakawa, tare da hukunce-hukunce marasa tausasawa. Kamar guture hancin mutum in ya karya dokar ‘kasa. Ya sa aka goge duk inda sunan Aten ko Akhanaten ya fito a Masar saboda a manta da shi har abada. A shekarar 1320BC ya mutu, daga nan Gidan Sarauta na 18 ya zo ‘karshe. Horembeb ba shi da magaji, saboda haka sai sarauta ta fa’da hannun wani maya ‘kinsa mai suna Paramesses. Wannan shi ne kakan kakan Fir’aunan Annabi Musa (AS). Ya cire Pa daga sunansa ya koma

Remesses I.

FIR’AUNA REMESSES II

Ramesses II dai shi ne wanda ake kyautata zatin cewa shi ne Fir’aunan da ya yi zamani da Annabi Musa (AS), wanda Allah Ya fa’di tarihinsa a cikin Al’kur’ani, littafin Allah mai tsarki. Kodayake masana irin su Maurice Bucaille suna ganin Merneptah ne ba Ramesses II ba. Saboda haka, ra’ayi ya banbanta ko tskanin Ramesses II da Merenptah wanene Fir’aunan Annabi Musa (AS). Wasu masanan Masar tadauri na ganin cewa Annabi Musa (AS) ya yi yayi da Remesses II ya kuma yi yayi da Merenmptah, wasu kuma na ganin dai-dai lokacin da Yahudawa suka yi ‘kaura daga Masar suka bi ta kogin Maliya, Merneptah ne ke kan karagar mulki. Sai dai ba bu cikakken bayani akan shi Merneptah kamar yadda ake da bayani akan Remesses II. To, kowane ne dai daga cikinsu Fir’aunan Annabi Musa (AS) Allah ne Ya fi tokowa sani. To amma dai duka gawawwakin na su suna nan, don haka, al}awarin Allah Ya cika kenan. A duba shafi na gaba domin ganin kyam kyamammun gawarwakin

Remesses II da Merneptah

Idan mun ‘dauka Remesses ne Fir’aunan annabi Musa (AS) to, kusan duk mai bin addinin Muslunci ko na Kiristanci ko Yahudu ya karanta a cikin littafinsu yadda Allah Ya bada labarin kafircin Fir’auna Remesses II. Saboda haka, ba za mu yi wani dogon bayani ba illa ‘dan tsokaci. Shi dai Remesses II ‘da ne ga Seti I wanda shi kuma ‘da ne ga Remesses I. Remesses I da sunansa Paramesses wanda asali ba jinin sarauta ba ne. Shi soja ne wanda ya gaji mulki Misra daga hannun Fir’auna Horembeb. Ya yi ya’ke-ya’ke da gine-gine manya katafarai. A ta’kaice dai za a iya cewa yana ‘daya cikin manyan masu mulki da Masar ta dauri ta ta’ba yi. Cikin katafaraen gine-gine da yayi, ana ‘daukar babban ‘dakin nan da girmansa ya kai murabba’in kafa 5800 kuma an yi masa rufi tsaf. A yau da yake a bu’de, in ka shiga ka ce a wani sararin daji kake. Har yau in ka ie Karnak da Abu Simbel za ka ga wasu daga cikin maka-makan gine-gine da ya yi. Cikin manyan matansa akwai Nefertari da Manefrure. Ya kuma auri uwarsa ya kuma  aure ‘diyansa mata guda uk`u. ‘diyansa sun kai 150, ‘dansa na 13 ne ya gaje shi shi. Sunansa Merneptah.

A shekarar 1881 aka gane ‘kyan ‘kyamammun gawarwakin wasu fitattun sarakunan Masar ta dauri na Sabuwar Masarauta a wani wuri da yanzu akan kira Kufa]ar Sarakuna watau Valley of the kings. Cikin gawarwakin har da ta Fir’auna Remesses II, saura sune Seti I da Ramesses I da Ahmose I da Amenhotep I da Thutmose I da Thutmose II da kuma Thutmose III.  Duka sai aka kai su gidan adana kayan tarihi na Masar. A cikin shekarar 1912 Masanin Masar ta dauri Eliot Smith ‘dan ‘kasar Ingila, ya fahimci cewa wata cuta ta kama gawar Remesses II saboda haka aka fara ‘ko’karin tsayar da ‘kwayar cutar dake neman ‘bata gawar. A cikin shekarar 1976 aka ‘dauki gawar zuwa ‘kasar Faransa don kyautata ta. Wannan shi ne karo na farko da gawar wani Fir’auna ta bar Masar. Da aka sauka da gawar a filin jirgin saman Orly, sai hukumomin Faransa suka yi mata tarba irin wadda ake yi wa Shugabannin {asashe har da shimfida jar darduma. Gawar Fir’auna Remesses II ta yi shekaru 3200 da binnewa, saboda haka ta fara fita daga hayyacinta. Don haka ne aka sa likitoci da masana kimiyya guda 102 ‘kar’kashin Farfesa Lionel Balout suka yi watanni bakwai suna aiki akan gawar. Bayan an gyatta ta sai aka maido ta Masar. Ai al’kawarin Allah ba ya tashi.

KAMMALAWA

A wurin kammalawa, ina ganin zai yi kyau in yi bayani a ta}aice bisa yadda ilmin Masar ta dauri ya iso mana. A nan ya kamata a fahimta cewa hanya ta farko ita ce ta Saukakkun Litttatafai kamar Al-qur’ani mai tsarki. Hanya ta biyu ita ce ta hanyar abubuwan tarihi da su Misrawan suka bar mana. Sai kuma hanya ta uku wadda ita ce ta bada cikakken bayani akan tarihin wayewar kan Masar ta dauri na tsawon shekaru dubu biyar zuwa bakwai. Wannan ita ce ta hanyar iya karanta, da fahimta da kuma fassara rubutunsu na dauri. A nan ya kyautu mu koma mu yi godiya ga masana na baya da suka yi }o}arin gano sihirin rubutun misrawan dauri, irin su Nicolas Claude Fabri da Athanasius Kircher da Bernard Montfaucon da Jean-jacques Barthelemy da Antione Isaac Silvetre. To amma mutum ]aya da za mu fi yi wa godiya shi ne ]an }asar Faransa Jean-Francois Champollion wanda ya shekara 30 yana }o}arin warware zaren ya kuma warware shi a }arshe. Sai kuma masanan Masar ta dauri da dama da suka yi bincike da rubuce rubuce a kan Wayewar kan Masar ta dauri irin su Manetho da Herodotus da Lepsius da Maspero da Marriette da Carter da Cheik Anta-Diop da su Gardiner da sauransu. Babu shakka, ba dominsu ba, da sai mu ce sai dai a yi kame-kame da shaci-fa’di.

To, babban abin burgewa da Masar ta dauri ta barwa ‘yan baya shi ne gine-gine. Duk da cewa su gine-ginen duwatsu suka yi, za mu iya cewa Misrawan dauri da na yau sun yi ‘ko’karin adana kayan tarihinsu, ba domin haka ba, da babu abin da zai rayu har mu ‘yan baya mu zo mu gane shi mu kuma ‘karu da shi. Don haka, kenan ya zama wajibi ga kowace irin wayewar kai ta adana kayan tarihinta domin ‘yan baya. Wannan ne ya sa na ga ya dace in nuna ba’kin cikina game da yadda mu a ‘kasar Hausa muke yin watsi tare da fatali da kayan mu na tarihi. Yanzu ku duba badalar Kano. Duk da cewa an gina ta ne lokacin sarakunan Ha’be, da jahadi ya zo ‘kar’kashin Fulani, ba su rusa ta ba. Da Turawa suka zo, ba su rusa ta ba. Amma bayan Turawa sun tafi, gata nan ta zama abin tausayi. Na tabbata nan da ‘yan shekaru ba za sami ko kufai na badala ba (sai shaguna?). Don haka, ina ganin lokaci ya yi da mutanen Kano za su fara wani motsi ko rugugi babba na gani cewa an tada badalar Kano. Kada ku ji komai, za a iya. Ku kuma ‘daliban Jami’a, ha’k’kin ku ne ku wayar da kan jama’a akan wannan harkar. Zan dakata anan sai kuma in mun sami wata dama za mu ]’dra. Na gode kwarai da kuka zo kuka saurare ni.

Soyez le premier à commenter

Poster un Commentaire

Votre adresse de messagerie ne sera pas publiée.


*