Dan sandan Indiya na fuskantar barazana don ya ceto Musulmi

Gagandeep Singh jami'in dan sanda

Yan sanda a Indiya sun ce jami’in dan sandan nan da ya sha yabo saboda jarumta da ya nuna lokacin da ya hana wani gungun mabiya addinin Hindu kona wani Musulmi, yana fuskantar barazana ga rayuwarsa.

Tauraruwar Gagandeep Singh, wanda jami’in dan sanda ne a jihar Uttarakhand ta haskaka bayan da aka wallafa hoton bidiyo da ya nuna lokacin da ya ceto wani Musulmin daga hannun wani gungun mutane a makon da ya gabata.

Mutumin ya kai ziyara ne wani wurin ibada na mabiya Hindu tare da budurwarsa wacce take bin addinin Hindu.

Gungun mutanen sun yi masa kawanya inda suka yi kokarin far masa, kuma sun zarge shi da « yin jihadi ta hanyar amfani da soyayya ».

Kalma ce da kungiyoyi masu tsatstsauran ra’ayin addinin Hindu suke amfani da ita wadanda suke zargin maza Musulmi da sauya ra’ayin mata mabiya Hindu ta hanyar soyayya.

Lokacin da bidiyon al’amarin ya fara bayyana a shafukan sada zumunta, mutane da dama sun kira Mista Singh « mutumin da za a yi koyi da shi  » kuma jaridu da dama a kasar sun wallafa labarin.

« Ina aikina ne kawai. Ko da ban sanya kayan sarki ba, zan yi abin da da na yi kuma ya kamata kowane Ba’indiye ya yi haka, » in ji shi.

Sai dai kuma ba da jimawa ba ne mutane suka fara sukar matakin da Mista Singh ya dauka, inda suke zarginsa da kare « sabuwar dabi’a ».

Jami’an ‘yan sanda da suke aiki tare da shi sun ce an rika tura masa sakonnin barazana ga rayuwarsa.

Sai dai wadansu ‘yan siyasa a bainar jama’a sun ce gungun mabiya Hindu ba su aikata laifi ba.

« Ba daidai ba ne maza Musulmi su rika zuwa da mata mabiya addinin Hindu zuwa wuraren ibadanmu duk da cewa sun san cewa wurin ibada ne, mai tsarki, »in ji Rakesh Nainwal, mamba a jam’iyyar BJP mai mulki.

Sai dai wadansu mazauna unguwar Ramnagar, inda a nan ne lamarin ya faru sun ce al’amarin yana tayar da hankali.

« Idan saurayi da buduwarsa sun je wani wuri tare, shin me ya sa kungiyoyin masu tsatstsauran ra’ayi za su kira shi da yin jihadi ta hanyar amfani da soyayya tare kuma da kai musu hari  » in ji Ajit Sahni, wani mazaunin Ramnagar.

Soyez le premier à commenter

Poster un Commentaire

Votre adresse de messagerie ne sera pas publiée.


*