Ba ni da ra’ayin shiga siyasa – Ali Nuhu

Fitaccen jarumin fina-finan Hausa Ali Nuhu, ya ce ba zai taba shiga harkokin siyasa ko tsayawa takara ba, duk kuwa da irin farin jini da daukakar da yake da ita.

A wata hira da ya yi da wakilin BBC na sashen Turancin Buroka, Mansur Abubakar, jarumin ya ce: « Ba ni da ra’ayin siyasa ko kadan, ni fim ne sana’ata ba siyasa ba. »

An kuma tambayi Ali Nuhu wanda suka yi hirar a yayin da suke daukar wani fim a Kano, ko zai iya shiga fina-finan kasar Amurka na Hollywood a nan gaba kamar yadda yake yin na Kudancin Najeriya?

« Ni duk fim din da ya biyo ta hanyata in dai an min tayinsa to zan shiga, in dai har ina jin harshen da za a yi fim din da shi, » a cewar jarumin.

Ya kara da cewa; Ga masu cewa ba sa ganina a baya-bayan nan a fina-finan Kudancin Najeriya, to sai dai idan ba sa kallon sabbin fina-finai ne don ba a dade ba ma na yi wani fim mai suna « Banana Island. »

Kula da iyali

An tambayi Ali Nuhu koyana samun isasshen lokacin da yake kula da iyalinsa ganin cewar sana’ar tasu mai cin lokaci ce?

Sai ya ce « Kwarai ina samun lokacin da nake zama da iyalina da kuma kula da su sosai, musamman a wannan lokaci na azumin watan Ramadan, tun da ba mu faye dadewa a wajen al’amuran daukar fim ba. »

Ali Nuhu ya kuma shawarci matasan Najeriya da su yi koyi da abokinsa Ahmed Musa, dan wasan tawagar kwallon kafa ta Najeriya, kan yadda yake taimaka wa marasa galihu a lokacin Ramadan a jihar Kano.

Soyez le premier à commenter

Poster un Commentaire

Votre adresse de messagerie ne sera pas publiée.


*